Back

Tinubu ya umurci biyan bashin fiye da Naira miliyan dari uku kudin wutar lantarkin fadar shugaban kasa 

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta biyan kudaden wutar lantarki miliyan dari uku da arba’,in da biyu da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya biyo fadar shugaban kasa.

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, ta bayyana cewa umarnin Tinubu ya biyo bayan sulhunta asusu ne tsakanin hukumar gudanarwar gidan gwamnatin Tarayyar da kamfanin rarraba wutar lantarki na AEDC.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ba kamar yadda kamfanin ya ce ya fara biyan bashin Naira miliyan dari tara da ashirin da uku a tallace-tallacen da aka biya a jaridu, kasafin kudin da ke gaban majalisar dokokin jihar ya kai N342, 352, 217.46, kamar yadda wata wasika da mahukuntan AEDC suka aike wa babban sakataren fadar shugaban kasa sanye da kwanan watan sha hudu ga watan nan.

“Bayan sulhunta matsayar da bangarorin biyu suka Yi, kuma suka gamsu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayar da tabbacin cewa za a biya AEDC bashin kafin karshen wannan makon.

Shugaban ma’aikatan ya ce biyan wannan bashin na fadar shugaban kasa, ya kasance abin misali ga hukumomi ya kuma bukaci sauran ma’aikatun gwamnati da su daidaita na su asusun na AEDC kuma su biya kudaden wutar lantarkin da ake bin su bashi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?