
Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce magajinsa, Bola Tinubu, ya taka rawar gani sosai tun bayan hawan sa mulki watanni tara da suka gabata.
Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, amma ya tabbatar da cewa Nijeriya ƙasa ce mai sarƙaƙiya wurin mulki.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, da jami’an gudanarwar hukumar NCS a garin Daura na jihar Katsina a ƙarshen mako.
Tinubu dai ya fuskanci suka sosai kan wasu manufofin sa na tattalin arziƙi da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma haɗe hanyoyin canjin kuɗi.
Waɗannan tsare-tsare da dai sauransu sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki, taɓarɓarewar tattalin arziƙi, da faɗuwar darajar Naira, wanda a ƴan kwanakin nan ya haifar da zanga-zanga.
Yayin da yake yi wa Adeniyi da tawagarsa jawabi, Buhari ya ce Nijeriya na da wahalar gudanarwa, inda ya umarci ƴan ƙasar da su jure wa matsalolin tattalin arziƙi da ake fama da su a ƙasar, tare da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci.
“Na gode ƙwarai da zuwan ku. Na yaba sosai. Ina tsammanin Tinubu ya yi ƙoƙari sosai,” in ji Buhari.
“Nijeriya tana da sarƙaƙiya sosai. Haƙiƙa, babu abin da kowa zai iya yi.”
Adeniyi, a nasa jawabin, ya godewa tsohon shugaban ƙasar kan rawar da ba a taɓa ganin irinsa ba wajen tallafawa Dokar NCS ta 2023.
Haka kuma CGC ta kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Daura, Mai Martaba Dakta Farouk Umar Farouk.
Adeniyi ya ce “Wannan matakin na doka ya bai wa hukumar NCS damar faɗaɗa ikon aiwatar da manufofin da ke da nufin ƙarfafa samar da kuɗaɗen shiga da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, hakan na ba da gudummawa sosai ga ci gaban tattalin arziƙin Nijeriya,”
Ya kuma yi magana game da manyan motoci dake ɗauke da kayan abinci da aka kama a kan iyaka, inda ya ce, “Zan kuma yi amfani da wannan dama domin yi muku bayani kan umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cewa duk motocin da ke jigilar kayan abinci da ke kan iyaka da hukumar Kwastam ta kama a mayar wa ƴan kasuwa tare da fatan za su dawo da su cikin kasuwannin Nijeriya.”
Idan dai ba a manta ba wannan ne karon farko da Buhari ya bayyana cewa Nijeriya aiki ce mai wahala ga shugabanni su mulka.
A watan Nuwamba 2023, yayin wata hira da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA), Buhari ya ce ƙasar na da wahalar mulka.
“Ƴan Nijeriya na da matuƙar wahala. Mutane sun san haƙƙinsu. Suna ganin ya kamata su kasance a wurin, ba ku ba. Don haka, suna lura da kusan kowane matakin ku. Kuma dole ne ku yi gwagwarmaya dare da rana don tabbatar da cewa kun cancanta sosai,” inji shi.