Back

Tinubu ya yi maraba da sakin ‘yan makarantar Kuriga, ya ce dole ne a samar da tsaro a makarantu domin koyo

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi maraba da labarin sakin ‘yan makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna, ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi domin samun sakamako mai kyau, musamman kan harkokin tsaro.

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, shugaban ya kuma yabawa Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, da hukumomin tsaro, da kuma gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan ƙwazon da suka gudanar da lamarin, yana cewa gaggawa, kulawa mai zurfi, da sadaukarwa maras gajiya suna da muhimmanci ga sakamako mafi kyau a lokuta na sace-sacen jama’a.

Tinubu ya kuma yi maraba da sakin ɗaliban wata makarantar Tsangaya da ke jihar Sokoto, inda ya yabawa duk ɓangarorin da suka yi wannan ƙoƙari.

Shugaban ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa na fitar da dabaru dalla-dalla don tabbatar da cewa makarantunmu sun kasance amintattun wuraren koyo, ba wuraren sace-sacen mutane ba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?