Back

Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a ofishin NSA

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin Ko’odineta na Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci (NCTC) da na Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Makamai Marasa Nauyi (NCCSALW).

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale, Mashawarci Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ngelale ya ce sabon Ko’odineta na NCTC shi ne Manjo Janar Adamu Garba Laka yayin da na NCCSALW shine DIG Johnson Babatunde Kokumo mai ritaya, dukkansu a ƙarƙashin Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar ya ce Laka ya yi ayyuka daban-daban a yankin Arewa maso Gabas, inda ya yi amfani da dabarun da suka ƙanƙantar da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ya ce Laka ya kuma yi aiki a Sierra Leone da Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Kwango a ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya kuma yana cikin tawagar Nijeriya a atisayen AFRICOM na Amurka a Senegal.

Ya yi Digirin Digirgir a Fannin Tsaro na ƙasa daga Jami’ar Tsaro ta Ƙasa a Pakistan, da kuma fannin Harkokin Ƙasa da Ƙasa da Nazarin Dabaru a Kwalejin Tsaro ta Nijeriya.

Ngelale ya ce Kokumo ƙwararre ne a fannin tabbatar da doka da oda tare da gogewa na sama da shekaru 30 a fannin rigakafin aikatawa, gudanarwa, tantancewa da kuma iyakance laifuka.

Ya ce Kokumo shi ne Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Sashin Bayanan Asiri da Binciken Manyan Laifuka na Rundunar a Hedikwatar Rundunar, Abuja, daga 2022 zuwa 2023.

Ngelale ya ce Shugaban Ƙasar ya yi hasashen sabbin waɗanda aka naɗa za su kawo ɗimbin gogewar da suka samu a cikin waɗannan muhimman ayyuka domin kawar da barazanar tsaro yadda ya kamata ta hanyar riga-kafi, sahihanci da ƙwazo.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?