Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Laraba ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Majalisar Dokoki ta ƙasa ne don ƙaddamar da tsohuwar taken Nijeriya, “Nigeria We Hail Thee.”
Ya ce Shugaban Ƙasar ya sanya hannu a kan dokar da ta mayar da Nijeriya ga tsohuwar taken ta ƙasa kamar yadda majalisun biyu suka amince da shi a ranar Laraba.
Ya ce Shugaban Ƙasar ba zai gabatar da jawabi a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokokin kamar yadda aka sanar a baya ba.
An shigar da Shugaban Ƙasar ne a lokacin gabatar da wannan rahoto.
Tinubu ya isa zauren majalisar ne tare da Shugaban Ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, da wasu mataimakan shugaban ƙasar.
Bayan isowarsa, aka rera tsohuwar Taken Ƙasar, “Nigeria We Hail Thee.”
Har ila yau waɗanda suka halarci zauren majalisar sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; tsohuwar mataimakiyar kakakin majalisar, Patricia Etteh; da tsoffin ‘yan majalisa.