Back

Tinubu zai buɗe taron ƙoli kan yaƙi da ta’addanci na Afrika a Abuja

Bola Ahmed Tinubu

A ranar Litinin 22 ga Afrilu, 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai buɗe Taron Ƙoli kan Yaƙi da Ta’addanci na Afrika a Abuja.

Nijeriya tare da goyon bayan Ofishin Yaƙi da Ta’addanci na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNOCT), na shirya wani taron ƙoli kan yaƙi da ta’addanci na Afirka mai taken, ‘Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Yanki da Gina Cibiyoyi don Magance Barazanar Ta’addanci’, a Abuja, daga 22 ga Afrilu zuwa 23 ga Afrilu.

Maƙasudin taron shi ne inganta haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci a ɓangarori daban-daban, da kuma sake fasalin yadda ƙasashen duniya ke ba da haɗin kai ga ayyukan ta’addanci a nahiyar Afirka, tare da jaddada mahimmancin hanyoyin warware matsalolin da ƙasashen Afirka suke da shi.

Taron dai zai samar da wani dandali na yin nazari kan yanayi da tsananin barazanar ta’addanci a nahiyar, da nufin cimma matsaya kan muhimman tsare-tsare da matakan shawo kan wannan annoba.

Har ila yau, taron zai zurfafa haɗin gwiwa a shiyyar, da ƙara habaƙa ƙarfin hukumomin ƙasashe mambobin ƙungiyar, da samar da damar yin musayar ayyuka mafi kyau da ilmi, don yaƙar barazanar ta’addanci a Afirka.

Ana sa ran shugabannin ƙasashe da na gwamnatoci da manyan jami’an gwamnati a faɗin Afirka, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da cibiyoyin ƙasa da ƙasa, da wakilan jami’an diflomasiyya, da na ƙungiyoyin farar hula za su halarci taron.

Amina Mohammed, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, za ta halarci taron.

Malam Nuhu Ribadu, Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, da Mista Vladimir Voronkov, Mataimakin Sakatare-janar kan Yaƙi da Ta’addanci, UNOCT, za su gabatar da jawabin ƙarshe a ƙarshen taron.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?