Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Legas a yau ranar Alhamis zuwa Doha a ƙasar Qatar don halartar taron kasuwanci da zuba jari a tsakanin Najeriya da Qatar.
Ziyarar ta kwanaki biyu na zuwa ne bisa gayyatar sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
Tinubu, wanda ya isa Legas jiya daga jihar Ondo, zai tashi ne bayan kaddamar da jirgin kasa na Red Line na Jihar ta Legas.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban kasar zai yi amfani da ziyarar wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama da suka hada da tsaro, musayar al’adu, da kuma bunkasar tattalin arziki.
Sanarwar ta ce, baya ga wasu shirye-shirye da gwamnatin Qatar ta tsara, shugaba Tinubu zai kuma halarci taron kasuwanci da zuba jari, wanda zai samu halartar ‘yan kasuwa na kasashen biyu.
A cewar shi: “Bisa gayyata da Mai Martaba, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, Sarkin Qatar, ya yi wa dhugabsn Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai bar jihar Legas, ya kuma kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Qatar ranar Alhamis 29 ga Fabrairu, 2024, don kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama da suka hada da tsaro, musayar al’adu, da bunkasar tattalin arziki.”
“A yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da suka mayar da hankali wajen bunkasa bangarori na Najeriya na hakika da kuma samar da jari mai amfani a fannonin kasuwanci, ilimi, al’adu, ma’adanai masu karfi, tattalin arzikin dijital, noma, da iskar gas da inganta hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci da dai sauran su.”
“Shugaban zai kuma halarci taron kasuwanci da saka hannun jari wanda zai hada manyan jami’an gwamnati a sassa masu zaman kan su da na gwamnatim Najeriya da Qatar don ciyar da damammaki dabam-dabam gaba domin samun ci gaban kasa da ci gaban juna.”
“Shugaban kasar zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati domin rattaba hannu kan yarjeniyoyi.”