Back

Tinubu zai halarci taron Tarayyar Afirka a Addis Ababa

A gobe Alhamis Sha biyar ga watan biyu na shekarar nan Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha domin halartar Taron Shugabannin Ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) karo na talatin da bakwai.

Taken taron na bana shi ne ”Koyar da ɗan Afirka yadda zai dace da ƙarni na ashirin da ɗaya: Gina tsarin ilimi mai ƙarko don ƙara samun ilimi mai tsawon rai, inganci, da kuma dacewa a Afirka”.

A cewar wata sanarwa Da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, a yau laraba, yace Shugaban Ƙasar zai bi sahun sauran shugabannin ƙasashen Afirka wajen gudanar da manyan tarurruka kan sauye-sauyen hukumomin Tarayyar Afirka, zaman lafiya da tsaro, batutuwa na musamman kamar sauyin yanayi, da kuma hanyoyin shiga da abubuwan da suka sa a gaba a Ƙungiyar Ƙasashe Ashirin (G20).

A wani gefen taron kuma, Shugaba Tinubu zai halarci wani babban taro na musamman na shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a matsayinsa na Shugaban ƙungiyar na yankin.

Shugaba Tinubu dai zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai dawo Abuja bayan kammala taron.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?