Back

Tinubu zai tafi Netherlands da Saudi Arabia ranar Talata

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

A ranar Talata, 23 ga Afrilu, 2024, Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, zai bar Abuja zuwa ƙasar Netherlands domin ziyarar aiki.

Shugaban Ƙasar zai kuma halarci taron Dandalin Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Afrilu a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Bisa goron gayyatar da Firaministan Ƙasar Netherlands, Mark Rutte ya yi masa, Shugaba Tinubu zai tattauna da Firaministan Ƙasar, kuma zai yi tarurruka daban-daban tare da Mai Martaba Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima na Masarautar.

“Yayin da yake ƙasar Netherlands, Shugaban Ƙasar zai halarci Taron Kasuwanci da Zuba Jari na Nijeriya da Dutch wanda zai haɗa shugabannin kamfanoni da ƙungiyoyi a ƙasashen biyu don gano damammaki na haɗin gwiwa, musamman a fannin noma da kula da ruwa wajen samar da sabbin hanyoyin samar da mafita mai ɗorewa na ayyukan noma.

“Za a kuma yi tattaunawa mai zurfi tare da jami’an Dutch game da ayyukan kula da tashar jiragen ruwa wanda suke da ƙwarewa da ta shahara a duniya.

“Bayan ayyukansa a Netherlands, shugaban zai halarci wani taro na musamman na Dandalin Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) wanda aka shirya gudanarwa a ranar 28-29 ga Afrilu a Riyadh, Saudi Arabia.

“A taron Dandalin Tattalin Arziƙin Duniya, wanda ya mayar da hankali kan Haɗin gwiwar Duniya, Ci gaba da Makamashi don Ci gaba, Shugaba Tinubu da muƙarrabansa za su yi amfani da damar taron na sama da shugabanni 1,000 daga kasuwanci, gwamnati, da jami’o’i don tattaunawa don ci gaban Ajandar sa ta Sabunta Fata ga ƙasar.”

Shugaban zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?