Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, zai bar Abuja, Babban Birnin Ƙasar, zuwa Legas a ranar Lahadi gabanin Ƙaramar Sallah.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Ngelale ya ce, “Don girmama bikin da za a yi, wanda ke nuna ƙarshen watan Ramadan, Shugaban Ƙasar zai yi amfani da lokacin wajen addu’a ga Nijeriya tare da iyalinsa.”
“Shugaban Ƙasar zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a lokacin bikin Ƙaramar Sallah da kuma bayan kammala bikin.