
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai tashi daga Abuja ranar Talata, zuwa Dakar na ƙasar Senegal domin bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
Mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ya bayyana cewa ziyarar shugaban na zuwa ne bisa gayyatar jamhuriyar Senegal.
Ya ce, Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) na Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci, zai bi sahun sauran shugabannin ƙasashen yankin domin halartar bikin ƙaddamarwar a cibiyar Diamniadio a ranar Talata.
Shugaban Ƙasar zai samu rakiyar Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ce ana sa ran Shugaban Ƙasa Tinubu zai dawo Nijeriya bayan kammala rantsar da shi.