
Tsohon Gwamnan Abia, Ogbonnaya Onu
Dakta Ogbonnaya Onu, tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma Ministan Kimiyya da Fasaha a gwamnatin Muhammadu Buhari ya rasu.
Wata majiya da ke kusa da marigayin ta tabbatar da rasuwar a ranar Alhamis.
Onu ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ba a bayyana ba a Nijeriya.
Ku tuna cewa marigayi tsohon ministan mai shekaru 72 a duniya ya fito takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar APC a zaɓen 2023, amma ya sha kaye a hannun Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Onu ɗan siyasan Nijeriya ne, marubuci kuma injiniya har zuwa rasuwarsa.
Shi ne gwamnan farar hula na farko a Jihar Abia kuma ya kasance Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire na Nijeriya daga watan Nuwamba 2015 har ya yi murabus a shekarar 2022.
Tsohon gwamnan ya kasance minista mafi daɗewa a ma’aikatar.