Back

Tsohon Ministan Ilimi, Gbagi ya rasu

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), a zaɓen da ya gabata a Jihar Delta, Olorogun Barr Kenneth Omemavwa Gbagi, FNIM OON, ya rasu.

Gbagi wanda tsohon ministan ilimi ne kuma masanin masana’antu ya rasu yana da shekaru 62 a duniya.

Babban masanin laifuka kuma babban lauyan ya rasu ne ranar Asabar, 4 ga Mayu, 2024.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban ɗansa, Cif Emuoboh Gbagi, a madadin iyalan Gbagi, ta tabbatar da mutuwarsa.

A cewar sanarwar “Abin baƙin ciki ne amma da godiya ga Allah, muna sanar da rasuwar masoyinmu mahaifinmu, kakanmu, mijinmu, kuma ɗan’uwanmu, Olorogun (Barr.) Kenneth Omemavwa Gbagi, FNIM, OON; Tsohon Ministan Ilimi, wanda ya rasu a ranar 4 ga Mayu 2024 yana da shekaru 62.

“Muna samun ta’aziyya a cikin abubuwan tunawa na rayuwarsa, nasarorinsa, da kuma tasirin da ya yi a rayuwar mutane da al’ummomi marasa adadi.

“Muna neman addu’o’inku ga danginmu a wannan lokaci na rashin. Allah ya sa ya huta”.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?