Back

Tubabbun ‘yan Boko Haram sun kai hari ofishin ‘yan sanda a Borno

Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram a daren ranar Talata sun kai hari ofishin ‘yan sanda a Maiduguri a ƙoƙarinsu na ‘yanto abokan aikinsu da aka kama bisa zarginsu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Sai dai Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno, Kenneth Daso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ofishin ‘yan sandan, ya ce jami’an da ke bakin aiki ne suka fatattaki maharan.

Daso ya ce an kai harin ne sakamakon wani samame da ‘yan sanda suka kai.

Ya ce, “A ranar 30/04/24 da misalin ƙarfe 1745 a aikin haɗin gwiwa a Kasuwar Fara, bayan wani rahoton sirri da aka samu cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi, masu shan taba, tubabbun ‘yan Boko Haram suna aikata munanan ayyuka, an kama mutum takwas, ciki har da maza guda bakwai da mace da gram 476 na haramtattun ƙwayoyi.

“Kamar yadda kuka sani gwamnatin jihar ta haramta irin waɗannan ayyuka a yankin tun shekarar da ta gabata.

“Sa’o’i kaɗan da kamasu, wasu marasa gaskiya, waɗanda ake kira tubabbun Boko Haram, sanye da kayan sojoji suka yi ƙoƙarin kutsawa ofishin ‘yan sanda da ke Ibrahim Taiwo, amma nan take aka fatattake su.

“Bayan nan, sai suka je suka kai hari kan Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da wurin binciken ababen hawa na Hukumar NDLEA bayan ƙofar maraba ta garin suka ƙona wurin,” inji shi.

ASP Kenneth ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi domin bankaɗo waɗanda ke da hannu wajen aikata wannan aika-aika.

Sai dai wasu shaidu sun shaida cewa maharan sanye da kayan sojoji ɗauke da adduna, sun shiga ofishin ‘yan sandan da ƙarfin tsiya inda suka tafi da wasu da ake zargin.

“Kusan 20 daga cikin maharan sun kutsa kai cikin ofishin ‘yan sandan inda suka tsere tare da wasu daga cikin mambobin da aka tsare.

“Sun bar wasu ‘yan sanda da ke bakin aiki da raunuka; sun kuma ci gaba da kai hare-hare kan masu wucewa da adduna,” inji shi.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce jami’an ‘yan sandan da ke ofishin sun yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin sun daƙile maharan amma suka ci ƙarfinsu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?