Back

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta sake yin kira da a yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu

Uwargidan Shugaban Ƙasa , Sanata Oluremi Tinubu, ta sake jaddada kiran ta ga ‘yan Majalisar Dattawa da su samar da dokar da za ta yanke wa masu satar mutane hukuncin kisa a ƙasar nan.

Ta sake nanata matsayin ne a ranar Alhamis a gidan Gwamnatin Tarayya lokacin da ta karɓi baƙuncin Sanatocin da ke wakiltar ƙananan hukumomin uku na jihar Legas.

Uwargidan Shugaban Ƙasar da ta taɓa wakiltar Legas na tsawon shekaru 12 a Majalisar Dattawa, ta yi kira ga ‘yan majalisar da su jagoranci aikin wajen samar da dokokin da suka shafi tsaro domin daƙile yaɗuwar wannan laifi.

“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta ƙuduri aniyar barin gado ga al’ummomi masu zuwa. Wannan yana buƙatar sadaukarwa da jajircewa,” inji ta.

Tun da farko, shugaban tawagar, Sanata Adetokunbo Abiru, mai wakiltar Legas ta Gabas, ya ce sun zo ne domin yi wa uwargidan Shugaban Ƙasa gaisuwar ban girma.

Airu, Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Kudu, ya ce sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya yi na kan gaba wajen ɗora al’ummar ƙasa kan turbar tattalin arziƙi da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ba da tabbacin cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da duba dokokin da suka shafi mutane musamman ta fuskar tattalin arziƙi da tsaro.

Airu ya bayyana fatansa na cewa nan ba da daɗewa ba al’ummar ƙasar za su zama matattarar tattalin arziƙi.

Sauran Sanatocin da suka kai ziyarar ban girma sun haɗa da, Wasiu Eshinlokun-Sanni, mai wakiltar Legas ta tsakiya da Dakta Oluranti Adebule mai wakiltar Legas ta Yamma.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?