Back

Wadanda suka yi garkuwa da Sarauniyar Kwara sun rage kuɗin fansa zuwa miliyan arba’in

 ’Yan bindiga da suka kashe Oba Olusegun Aremu-Cole, Olukoro na Koro-Ekiti a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara tare da yin garkuwa da matarsa ​​da wani mutum a daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata sun rage kuɗin fansa na N100m da suka saka wa waɗanda suka sace.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun tuntuɓi iyalan sarkin ne a ƙarshen mako domin biyan kuɗin fansa N100m, wanda a yanzu an rage zuwa N40m domin sako mutanen biyu da suka yi garkuwa da su bayan tattaunawa da iyalan.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargi ne suka kashe Oba Olusegun Aremu-Cole a fadarsa a daren ranar Alhamis yayin da aka yi awon gaba da matarsa ​​da wani mutum guda.

Shugaban Kwamitin Aiwatar Da Miƙa Mulki (TIC) a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, Kehinde Bayode, ya shaida wa wannan jarida ta waya cewa an kama wani da ake zargi a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar ranar Lahadi.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce “masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalin suna neman kuɗin fansa N100m wanda a yanzu aka rage zuwa N40m”.

Sai dai Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ya ce ba a yi kame ba dangane da lamarin.

“Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tura tawaga zuwa Koro Ekiti domin kamo waɗanda suka aikata laifin. Jami’an ‘yan sanda na aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a yayin faruwar lamarin. Har yanzu ba a yi kame ba. Za mu sanar da ku game da ci gaban da aka samu,” inji Ejire-Adeyemi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?