Back

Wani ɗan Kaduna ya buƙaci Naira miliyan 7 daga matar shi kafin ya sake ta

A ranar Alhamis ne wani ma’aikacin gwamnati a Jihar Kaduna, Jamilu Zuntu, ya buƙaci matar shi Hadiza Aliyu da ta biya shi Naira miliyan bakwai, domin ya biya mata buƙatar ta da take nema “ya sake ta.”

Hadiza na neman a raba auren ta da mijinta Jamilu da aka daura shekaru uku baya a wata kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna.

Jamilu, ya shaidawa kotun cewa ya kashe Naira miliyan biyu a hidimar karatun ta a cikin sama da shekaru biyu da rabi na auren su. “Na kuma sayi akwatunan tufafi na Naira miliyan biyu da rabi, kuma na kashe kudi a kan wasu bukukuwan gargajiya da aka yi.”

Hadiza, yayin da take mayar da martani kan buƙatar mijin na ta, ta ce a shirye take ta biya naira dubu dari, sadakin da Jamilu ya biya domin auren ta, “dan na samu ‘yanci daga wannan auren.”

Hadiza wacce lauyanta A. A. Imam ta wakilta, ta kuma roƙi a bata riƙon ‘yar su ‘yar shekara biyu da haihuwa, kamar yadda ta ce, “mahaifin ba shi da halin ciyar da ita.”

Alƙalin kotun, Isiyaku Abdulrahman, bayan ya saurari ɓangarorin biyu, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar ashirin da bakwai ga watan nan domin yanke hukunci.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?