Back

Wani mutum ya banka wa masallaci wuta yayin da ake sallah a Kano

Wani mutum ɗan shekara 38 mai suna Shafi’u Abubakar a ranar Laraba ya banka wa wani masallaci wuta a lokacin da ake sallah a unguwar Gezawa da ke Jihar Kano.

Blueprint ta ruwaito cewa Abubakar ya kulle masallacin, ya watsa man fetur, sannan ya banka wa masallacin wuta a lokacin da masallata ke yin sallar Asuba a cikin masallacin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya ce sun kama wanda ake zargi da aikata laifin, inda ya ce kawo yanzu ba a samu rahoton wani ya mutu ba.

SP Haruna ya bayyana cewa wanda ake zargin ya ce ya ɗauki matakin ne domin ɗaukar fansa kan mutanen da suka ha’ince shi a lokacin rabon gado.

Sai dai ya ce an killace wurin da lamarin ya faru, kuma an kwashe mutane ashirin da hudu (24) da suka haɗa da manya maza 20 da yara maza 4, aka garzaya da su asibitin Murtala Mohammed Kano, inda a yanzu haka suke samun kulawa.

A cewarsa, “Yau 15/05/2024 da misalin ƙarfe 0520 na safe, an samu rahoton cewa wani abu ya fashe a wani masallaci da ke ƙauyen Gadan da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Jihar Kano, a lokacin sallar Asuba, kuma wasu sun samu raunuka.

“Bayan samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, nan take ya tura tawagar rundunar ‘yan sandan da suka haɗa da ƙwararru a fannin kawar da bama-bamai ƙarkashin jagorancin CSP Haruna Isma’il da sauran ‘yan sandan da suka shafi laifuka ƙarƙashin jagorancin Jami’in ‘Yan Sanda na Reshe (DPO), reshen Gezawa, CSP Haruna Iliya.

“An killace wurin, kuma an kwashe mutane ashirin da hudu (24) da suka haɗa da manya maza 20 da yara maza 4 aka garzaya da su Asibitin Murtala Mohammed Kano, inda a yanzu haka suke samun kulawa.

“An gano wanda ake zargin kuma an kama shi; Shi ne Shafi’u Abubakar, mai shekaru 38, ya ce abin da ya yi na adawa ne kawai bayan rashin jituwar iyali na tsawon lokaci kan rabon gado, wanda waɗanda ya yi zargin cewa sun yi masa maguɗi suna cikin masallaci a lokacin, kuma ya aikata hakan. domin a ji muryarsa.

“Yayin da wanda ake zargin a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda, ana ci gaba da gudanar da bincike dalla-dalla kuma za a sanar da jama’a nan gaba kaɗan,” inji SP Haruna.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?