Wani mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, Mista Olukoya Ogungbeje, a ranar Litinin ya shigar da ƙara a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan kamfanonin sadarwa a Nijeriya, yana ƙalubalantar toshe layukan waya na ‘yan ƙasar da suka yi kwanan nan.
Mai ƙarar ya haɗo da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC); Babban Jami’in Hukumar, Dakta Aminu Mada; da kamfanin MTN a matsayin waɗanda yake ƙarar.
Sauran masu amsa ƙarar su ne Airtel, Globacom, da 9Mobile.
A cikin takardar ƙarar, Mista Ogungbeje ya tabbatar da cewa a wani lokaci a watan Janairu, waɗanda yake ƙara sun yi barazanar kashe layukan wayar ‘yan Nijeriya waɗanda ba su haɗa layukan wayar su da lambar shaidar su ta Ƙasa, wato NIN, ba.
Ya ƙara da cewa bayan wannan barazanar, ya garzaya kotu inda ya samu umarnin kotu a ranar 22 ga Fabrairu na hana waɗanda ake ƙarar kashe layukan wayar ‘yan Nijeriya har sai an yanke hukunci.
Mai shigar da ƙarar ya ce ya yi mamakin gano cewa a ranar 28 ga Fabrairu, waɗanda yake ƙarar sun toshe masa layukan wayarsa da na ‘yan Nijeriya da dama, wato ƙi bin umarnin kotu.
Don haka, yanzu yana neman a bayyana cewa matakin da waɗanda ake ƙara suka ɗauka na toshe layukan ‘yan Nijeriya daga ranar 28 ga Fabrairu har zuwa yau, duk da umarnin kotu, kuskure ne kuma ba bisa ƙa’ida ba.
Yana neman a ayyana cewa kasancewar doka ce ta samar da waɗanda ake ƙarar, suna ƙarƙashin kotun shari’a da ikonta na shari’a, kuma wajibi ne su yi biyayya ga kotu.
Saboda haka, ya nemi umurnin kotu na barin duk wani mataki na haramta layukan wayar ’yan Nijeriya.
Mai ƙarar ya kuma buƙaci a ba da umarni ga waɗanda yake ƙara da su gaggauta buɗe layukan wayar ‘yan Nijeriya da abin ya shafa.
Ya nemi zunzurutun kuɗi har naira biliyan 10 daga kamfanonin sadarwa a matsayin diyya saboda toshe layukan waya na ‘yan Nijeriya da suka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma buƙaci a ba da umarni na dindindin da zai hana masu amsa ƙarar ɗaukar wasu matakai kan ‘yan ƙasar da abin ya shafa.
Ba a tsayar da ranar da za a saurari sabuwar ƙarar tasa ba.