Back

Wani mutum ya shiga hannun ‘yan sandan Kano bayan ya yi yunƙurin kashe kansa

An kai wani mutum da har yanzu ba a tantance ko shi waye ba wurin ‘yan sanda a Kano bayan da ya yi yunƙurin shaƙe kansa.

An dai gano cewa an gano mutumin ne a kan titin jihar, mita kaɗan daga gidan gwamnatin jihar.

A cewar masu wucewa, wasu ‘yan baranda da ba a san ko su waye ba ne suka yi yunƙurin shaƙe mutumin da kebul, amma ‘yan sanda sun musanta wannan iƙirarin.

An ce an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase (MAWTH) domin samun kulawar gaggawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a ranar Talatar da ta gabata ne aka kai mutumin wurin ‘yan sanda, kuma bayan sun duba shi ya amsa cewa shi ya ɗaure igiyar a wuyansa.

“Bayan mun kai shi asibiti, ya faɗi gaskiya. Ba a karɓi komai daga gare shi ba. Hasali ma shi ya ɗaure kansa da igiyar. Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda,” Kiwaya ya rubuta a shafinsa na Facebook.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?