
Ministar Abuja yayin da take jawabi a ma’ajiyar
Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya (FCT), Mariya Mahmoud, a ranar Litinin ta bayyana cewa sace-sacen da wasu ‘yan tada zaune tsaye suka yi a wata ma’ajiyar kaya a Gwagwa-Tasha a jiya ya wuce batun yunwa, laifi ne.
Ministar ta bayyana hakan ne a ƙarshen ziyarar da ta kai a Gwagwa-Tasha domin tabbatar da irin ɓarnar da aka yi a ma’ajiyar.
Da take zantawa da manema labarai a wurin, Hajiya Mariya ta bayyana abin da ta gani a matsayin wani lamari mara daɗi, lamarin da ya sa ‘yan tada zaune tsaye suka kwashe duk wani hatsi da sauran kayan abinci, ciki har da kwanon rufin da shinge.
Duk da yake ministar ta nuna rashin jin daɗin ta kan halin da matasan yankin ke ciki, ta ba da tabbacin cewa hukumar za ta samar da ofishin ‘yan sanda a dukkan ma’ajiyar gwamnati da ke faɗin yankin.
Idan dai za a iya tunawa, an yi tashe-tashen hankula yayin da wasu matasa suka kutsa kai cikin wani wurin ajiyar kayan gwamnati da ke garin Gwagwa na Gundumar Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da kayan abinci.
Wasu mazauna unguwar sun ce wasu matasa da yawa sun kutsa cikin ma’ajiyar da ke kewayen unguwar Tasha da misalin ƙarfe 7 na safe, inda suka yi awon gaba da buhunan masara da hatsi.
Kimanin mutane 15 ne ‘yan sanda suka kama da yin wannan aika-aika tare da ƙwato wasu kayayyaki masu daraja daga hannun su.
Ministar ta ce: “Mun zo nan ne sakamakon wani mummunan al’amari da ya faru da sanyin safiyar jiya, inda ‘yan tada zaune tsaye suka kai hari a wannan ma’ajiyar kuma suka kwashe duk wani abu da ke nan, ciki har da shinge.
“Ba kawai kayan abinci da ke nan ba, har da rufin, tagogi, da ma ƙofofin wannan wuri da ofisoshi duk an kai harin.
“Ku na iya ganin ta’adin. Babu wani abu da ya rage a nan, ciki har da nau’ikan injinan da ake amfani da su don sarrafa waɗannan abubuwa.
“Kamar yadda ku ka ji, ana zargin mutanen da ke kusa da su, matasan al’ummar ne suka haddasa wannan lamarin. Don haka, wannan lamari ne mai ban-haushi. Kuma ba mu ji daɗin hakan ba”.
Ministar ta bayyana cewa wannan abin takaicin ya faru ne a lokacin da hukumar ke zuba kayan abinci a ma’ajiyar ta domin cika umarnin mai girma Shugaban Ƙasa na a raba kayan abinci ga ɗaukacin ƙananan hukumomi shida na FCT.
Ta sha alwashin cewa hukumar za ta gurfanar da waɗanda suka aikata wannan mugun aiki a gaban kotu.
A cewar ta: “Mun yi rabo kusan sau biyu, sannan kuma ana gab da yin na uku. Waɗannan manyan motocin sun zo ne domin sauke waɗannan kayan abincin, sannan aka kai masu hari, har ma da raunata wasu da ke bakin aiki.
“Haƙiƙa wannan mummunan lamari ne. Kuma ba abu ne da gwamnati za ta yi wasa da shi ba. Duk waɗanda ke da hannu a ciki dole ne a gurfanar da su a kotu. Dole ne mu yi wani abu.
“Haka kuma, wannan alama ce da ke nuna cewa muna buƙatar ƙarfafa yanayin tsaro a duk wuraren ajiyar mu saboda dole ne a ajiye abinci.
“Amma yadda wannan abu ya faru a zahiri ya wuce yunwa. Wannan laifi ne. Wani da yake jin yunwa ba zai iya fita don cire duk rufin da ke nan ba. Duk ƙofofi, da tagogi duka.
“Wannan ba ya nuna cewa mu jakadu ne nagari na ƙasa. Don haka tabbas za mu ɗauki mataki kan wannan lamari da ya faru”.
Mariya Mahmoud ta jaddada cewa lamarin na iya kawo tsaiko wajen rabon kayayyakin jin daɗin jama’a a yankin, tana mai cewa, “Dole ne mu sake ginawa, ba kawai gyara wannan ma’ajiyar ba, da dukkan ofisoshin da ƙofofin da aka lalata.”