Wasu da ake zargin matsafa ne sun kashe wata mata mai matsakaicin shekaru a garin Osogbo na jihar Osun, tare da fille kan ta.
Bincike ya nuna cewa matar da aka kashe ta shafe wasu watanni ba ta da matsuguni a Oke-bale kuma an kai ta bayan shagunan daura da sakatariyar ƙaramar hukumar Osogbo inda aka yanka ta.
Maharan sun kuma yanke hannayenta biyu tare da watsar da gawar ta a filin da babu kowa a yankin.
Wasu ’yan kasuwa a yankin da suka so buɗe shagunansu, a safiyar Talata, sun gano gawar matar, inda nan take suka koma gida saboda tsoron kada jami’an tsaro su kama su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an fara bincike.