Wasu da ake zargin ‘yan ta da zaune tsaye ne sun kashe wani mai daukar hoto mai zaman kansa dan shekaru talatin da uku, Zacchaeus Salawadeen, bayan sun daddaba masa wuka a gaban ‘ya’yan shi uku.
An ce sun bi sawun Salawadeen har gidan shi da ke unguwar Tundun Fulani a Minna, babban birnin jihar Neja inda suka kashe shi har lahira.
An ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata bayan mai daukar hoton ya kammala aikin shi na ranar kuma ya nufi gida domin ya kasance tare da iyalan shi.
An garzaya da shi asibitin kwararru na IBB inda likitoci suka tabbatar da rasuwar shi daga kawo shi.
A cewar daya daga cikin mazauna yankin, maharan sun mamaye gidan Salawadeen bayan da suka shiga gidan shi suka kashe shi.
An kuma ce wadanda ake zargin sun kulle sauran mutanen gidan a wuri guda kafin su kutsa cikin falon Salawadeen su kashe shi.
Rahotanni sun bayyana cewa sun tafi da wasu kayayyaki masu daraja irin su kwamfutar tafi-da-gidan ka da kyamarar mamacin..
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an samo wasu hujjoji a wurin da lamarin ya faru yayin da aka fara bincike.