Back

Wasu ‘yan bindiga sun sace ɗan jarida na gidan talabijin na Channels a Rivers

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani ɗan jarida da ke aiki da gidan talabijin na Channels a Jihar Rivers, Joshua Rogers, a gidansa da ke Rumuosi a ƙaramar hukumar Obio/Akpor a jihar.

An sace Rogers ne a daren ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9 na dare bayan da aka ce an bi sawunsa zuwa gidansa bayan ya tashi daga aiki.

Rahotanni sun ce maharan sun tare shi da bindiga, inda suka tafi da shi a cikin motarsa.

Rogers, wanda shi ne wakilin Gidan Gwamnati na gidan talabijin na Channels, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne ya bayar da rahoton wani taron da aka gudanar a garin Ndoni da ke ƙaramar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni na jihar, inda Gwamna Siminalayi Fubara ya ƙaddamar da wata cibiyar kula da lafiya da tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Peter Odili, ya gina kuma ya bayar da gudummawa ga jihar.

An ruwaito cewa ɓarayin sun tuntuɓi matarsa, inda suka buƙaci a biya su naira miliyan 30.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?