Back

Wata baƙuwar cuta ta kashe mutane 4 a Zamfara, gwamnati ta gano mutane 177 da suka kamu da cutar

Kwamishinar Lafiya ta Jihar Zamfara, Dakta Aisha M.Z. Anka, ta tabbatar da ɓullar wata cuta da ba a san ta ba a jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya, Bello Ibrahim Boko, ya fitar ranar Juma’a a Gusau.

Sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatar ta gano aƙalla mutane 177 da suka kamu da cutar, kuma daga cikin yaran da abin ya shafa, huɗu sun mutu.

Dakta Anka ta bayyana cewa ciwon “yana da alaƙa da kumburin ciki, tarin ruwa a cikin ciki, haɓakar hanta, ƙara girma, zazzaɓi da raunin jiki gabaɗaya.”

“An samu ɓullar cutar a ƙananan hukumomin Maradun, Shinkafi, da Gusau a jihar. Yara sun fi kamuwa da cutar kuma ana alaƙanta lamarin da shan ruwa,” inji ta.

Ta ƙara da cewa “tuni ma’aikatar ta kai rahoton lamarin ga abokan hulɗar NCDC da duk masu ruwa da tsaki domin su shiga tsakani.”

“A halin yanzu ma’aikatar tana kan matakin bayar da agajin gaggawa don gano cututtukan, musabbabinsu da kuma shawo kan yanayin.

“Samfurin halittu iri-iri na mutane da na dabbobi, samfurin ƙasa, samfurin ruwa, samfurin noma da kayan abinci ana kai su daƙunan gwaje-gwajen Legas da Abuja don bincike.

“Ma’aikatar za ta ci gaba da sanar da jama’a da duk abokan hulɗar da suka dace game da duk wani sabon binciken don mayar da martanin gaggawa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?