Gwamnatin Jihar Sokoto ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ɗauki kan wata baƙuwar cuta da ta kashe yara uku a ƙaramar hukumar Isa ta jihar.
Da yake jawabi a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate da Babban Jami’in Gudanarwa na Ƙungiyar Maganin Rigakafi ta Duniya (GAVI), Dakta Sania Nishtar, a jihar a ƙarshen mako, Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Idris Gobir, ya ce yara 127 sun riga sun kamu da cutar.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta mayar da martani kan wannan lamarin ta hanyar tura tawagar ƙwararru zuwa yankin domin gudanar da bincike.
“Don haka muna neman Gwamnatin Tarayya ta sa baki domin daƙile cutar daga ci gaba da yaɗuwa,” inji shi.
Gobir ya jaddada ƙudirin su na inganta harkar rigakafi da inganta ayyuka a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar.
“Jihar ta duƙufa. Ba ma wasa da wani abu da ya shafi kiwon lafiya. Na san muna da mummunan tarihi idan aka zo batun rigakafin amma abu ne da muka gada daga gwamnatin da ta gabata.
“Muna aiki da gaske tare da sauran abokan tarayya don canza labarin. Za mu aiwatar da dukkan shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na kawar da cutar shan inna,” ya tabbatar.
Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Sakkwato, Dakta Larai Aliyu Tambuwal, ta tabbatar da cewa yara uku ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Tun da farko, Pate ya nemi ƙarin hanyoyi da haɗin gwiwar inganta ayyukan rigakafi a Sokoto.
A nasa ɓangaren, Nishtar ya bayyana cewa sun je jihar ne domin haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin fahimtar yadda za a inganta harkar rigakafi a jihar.