Back

Wata kotu ta bada umarnin korar Sarki Sanusi

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma umarci ‘yan sanda da su tabbatar an ba da duk wani haƙƙi da alfarma da ya kamata a ba Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero.

An tsige Bayero ne a makon da ya gabata bayan amincewa da ƙudurin dokar Masarautun Kano da aka yi wa gyara, kuma daga ƙarshe Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shi.

Alƙalin kotun, Mai shari’a S. A. Amobeda, wanda ya bayar da umarnin a ranar Talata ya bayyana cewa an ba da umarnin ne domin tabbatar da adalci da wanzar da zaman lafiya a Kano.

Umurnin ya ce, “An ba da umarni na wucin gadi da ya hana waɗanda ake ƙara ko dai su kansu, wakilansu, bayinsu, masu zaman kansu ko wani mutum ko wata hukuma gayyata, kamawa, tsarewa, barazana, tsoratarwa, musgunawa mai ƙara, kai samame ko ziyartar mai ƙara domin kamawa ko tauye haƙƙinsa ko ta wata hanya ta daban ko yunƙurin tauye haƙƙoƙin mai ƙara har sai an saurare ƙarar da kuma yanke hukunci.

“Umarnin hana waɗanda ake ƙara na 3 da na 4 da na 5 da duk sauran waɗanda ake ƙara hana mai ƙara ya yi amfani da gidansa da fadarsa da ke Fadar Sarkin Kofar Kudu da kuma samun duk wani haƙƙi da alfarma da aka same shi ta hanyar kasancewarsa Sarkin Jihar Kano da kuma korar duk wanda ke zaune a cikin fadar ba bisa ƙa’ida ba har sai an saurare ƙarar da kuma yanke hukunci.”

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga Yuni, 2024.

Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan wata Babbar Kotun Jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarnin hana korar Sarki Sanusi II.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?