Back

Watanni 8 ɗina a kan mulki ya fi shekaru 8 da ka ɓarnatar, inji Gwamna Abba ga Ganduje

Gwamna Abba da Ganduje

A jiya ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayarwa magabacinsa Abdullahi Umar Ganduje martani kan iƙirarin gazawarsa wajen gudanar da mulki, inda ya ce Gwamna Ganduje ya gaza a shekaru takwas da ya yi a kan mulki.

Gwamna Ganduje, wanda shi ne Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta ƙasa a yanzu, ya zargi Gwamna Yusuf da yin amfani da dabarun karkatar da hankulan jama’a don ɓoye gazawarsa wajen gudanar da ayyukansa a jihar.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran sa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya ce gwamnan yana karkatar da hankulan jama’a daga cewa “babu wani abu a ƙasa” a jihar da zai tabbatar da ƙarin kuɗaɗen da ake baiwa jihar tun daga farko gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya na mai da martani ne kan matakin da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka na gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da karɓar cin hancin dala 413,000, da kuma naira biliyan 1.38.

Amma Gwamna Yusuf, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a jiya, ya ce shekaru takwas da Gwamna Ganduje ya yi na da nasaba da cin hanci da rashawa, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma sayar da kadarorin gwamnati.

Ya ce, “Watanni takwas da muka yi a kan mulki sun zarce shekaru takwas da Ganduje ya ɓarnatar. Muna so mu sake jaddada ƙudiri da shirin gwamnatin yanzu na sanya duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa ya fuskanci fushin doka kan laifin da ya aikata da gangan.

“Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta jaddada cewa za ta bi diddigin badaƙalar faifan bidiyon dala har zuwa ƙarshe mai ma’ana. Don haka ya buƙaci a saki binciken ƙwaƙwaf da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFFC) ta gudanar a kan ‘Gandollar saga’ a shekarar 2018, domin ganin jama’a.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?