Back

Wike ya bai wa Shugaban Ƙasar Senegal takardar shaidar zama ɗan ƙasa ta Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa Shugaban Ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, takardar shaidar zama ɗan ƙasa ta Abuja, a lokacin da ya kawo ziyara Nijeriya.

Da yake maraba da Shugaban Ƙasar Senegal ɗin a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Alhamis a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Ministan ya kuma gabatar masa da mabuɗin alama na birnin.

A cewar Ministan, mabuɗin ya baiwa Shugaban Ƙasar Senegal duk wani haƙƙi da alfarma na ɗan ƙasa, kuma alamar girmamawa ne ga ƙaƙƙarfan abota da kyakkyawar alaƙar dake tsakanin Nijeriya da Senegal.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?