Back

Yaƙi a Gaza: An kai hari ma’ajiyar kayayyakin agaji, da yawa sun raunata, inji Majalisar Ɗinkin Duniya

UNRWA

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu, (UNRWA), ta ce an “kai hari” ɗaya daga cikin ma’ajiyar kayayyakin agaji da ke yankin zirin Gaza a ranar Laraba, inda ya raunata mutane da dama.

Mai magana da yawun hukumar, Juliette Touma, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa, (AFP), cewa, “Za mu iya tabbatar da cewa an kai hari a wata ma’ajiyar kayayyaki na UNRWA a Rafah (kudancin Gaza),” inji kakakin hukumar, Juliette Touma, inda ta ƙara da cewa “da yawa sun raunata.”

“Har yanzu ba mu da ƙarin bayani kan ainihin abin da ya faru ko adadin ma’aikatan UNRWA da abin ya shafa,” inji ta.

“UNRWA tana amfani da wannan wurin don rarraba abinci da ake buƙata da sauran kayan ceto ga mutanen da suka rasa matsugunansu a kudancin Gaza.”

Ma’aikatar lafiya a yankin Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce mutane huɗu ne suka mutu a wani “harin bam da aka kai a ma’ajiyar kaya.”

Wani mai ɗaukar hoto na AFP ya ga waɗanda lamarin ya rutsa da su suna isa asibitin Al-Najjar da ke Rafah, kuma aƙalla ɗaya daga cikin su ma’aikacin Majalisar Ɗinkin Duniya ne.

Lamarin na ranar Laraba ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da taɓarɓarewar yanayin jin ƙai a Gaza, inda Isra’ila ke gudanar da ayyukan soji tun watan Oktoba da nufin kawar da ƙungiyar ta Hamas.

Yaƙin dai ya samo asali ne sakamakon harin da Hamas ta kai a kuɗancin Isra’ila wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160, galibi fararen hula, a cewar wani alƙaluman jami’an Isra’ila na AFP.

Gangamin soji na ramuwar gayya na Isra’ila a Gaza ya kashe aƙalla mutane 31,272, galibi mata da yara, a cewar ma’aikatar lafiya a yankin da Hamas ke mulki.

Ya zuwa ranar 4 ga Maris, an kashe ma’aikatan UNRWA 162 tun farkon yaƙin Isra’ila da Hamas.

Mummunan ƙarancin abinci a Gaza bayan yaƙin sama da watanni biyar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27 daga rashin abinci mai gina jiki da rashin ruwa, yawancinsu yara ne, inji ma’aikatar.

Jami’an agajin sun ce wasu tsauraran matakan da jami’an tsaron ƙasar Isra’ila ke yi kan duk wani kaya da ke shiga yankin na kawo tsaiko wajen kai kayan agaji, sannan ana mayar da wasu manyan motocin dakon kaya idan aka gano suna ɗauke da kayayyakin da aka haramta.

Hukumomin Isra’ila sun ce an samu tarnaƙi ne sakamakon tarin kayan agaji a ɓangaren Falasɗinu saboda babu isassun motocin da za su raba kayan kayan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?