Back

Yaƙi a Gaza: Harin jirgin sama ya kashe ‘yan uwa 36 da suke shirye-shiryen azumi

A sakamakon harin bam da Isra’ila ke kaiwa wanda ya raba su da muhallansu, iyalan Tabatibi sun taru a Gaza ta tsakiya domin cin abinci tare a daren Juma’a na farko na watan Ramadan, lamarin da ya rikiɗe zuwa zubar da jini.

Wani hari ta sama ya afkawa ginin da suke zaune a lokacin da mata ke shirya abincin sahur, inda ya kashe ‘yan uwa 36, ​​kamar yadda wasu da suka tsira suka shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran AFP a ranar Asabar.

Ma’aikatar Lafiya a Gaza ta Hamas, wacce ta bayar da adadin waɗanda suka mutu, ta ɗora wa Isra’ila alhakin harin da aka kai a Nuseirat, yayin da sojojin Isra’ila suka ce suna duba lamarin.

“Wannan ita ce mahaifiyata, wannan mahaifina ne, wannan gwaggo ta ce, kuma waɗannan ‘yan’uwana ne,” Mohammed al-Tabatibi ɗan shekara 19, wanda hannunsa na hagu ya ji rauni a harin, ya faɗa cikin hawaye a Asibitin Shahidai na Al-Aqsa dake Deir al-Balah.

“Sun jefa bam a gidan a lokacin da muke ciki. Mama na da inna ta suna shirya abincin suhur. Dukkansu sun yi shahada.”

Ya yi maganar ne a lokacin da aka baje gawarwaki a harabar asibitin, sannan aka jera su a kan wata babbar mota da za a kai su wata maƙabarta.

Saboda babu isassun jakunkuna na gawa, wasu daga cikin waɗanda suka mutu – ciki har da aƙalla yara biyu – an nannaɗe su da farin ƙyalle mai ɗauke da jini, faifan gidan talabijin na AFP ya nuna.

Harin na Nuseirat na ɗaya daga cikin “mummunan hare-hare ta sama” guda 60 da ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Hamas ya bayar da rahoto a cikin dare, daga birnin Gaza da ke arewa zuwa Rafah a kudancin ƙasar.

“Wannan dare ne na zubar da jini, dare na zubar da jini sosai,” inji Salama Maarouf na ofishin yaɗa labaran gwamnati da Hamas ke gudanarwa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?