Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang; mai kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana; da sauransu sun ce dole ne Nijeriya ta tabbatar da cewa waɗanda suka lashe zaɓe na gaskiya sun bayyana gabanin rantsarwa.
Sun bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na Gidauniyar Haske Satumari mai taken, “Sake Fasalin Zaɓe da Shari’a: Muhimmancin Dimokuraɗiyya, Mulki, Shugabanci da Tsarin Zaɓensa,” wanda aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Gwamna Mutfwang, wanda ya nuna damuwarsa kan hukuncin kotu daban-daban kan ƙararrakin zaɓen 2023, ya ce tun da shugabanci ya zama muhimmi, bai kamata ba a bar alƙalai da lauyoyi su yanke hukunci kan wanda ya lashe zaɓe na gaskiya ba.
Wani Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, ya yi zargin cewa da gangan wasu lauyoyi a Nijeriya suke yi wa tsarin zagon ƙasa, yana mai jaddada cewa kada ‘yan Nijeriya su bar lauyoyi da alƙalai su yanke hukunci kan wanda aka zaɓa.
“Alƙalai ba su dace da ƙayyade wanda ya ci zaɓe ba saboda ba sa wurin. Ya kamata al’umma su ƙayyade wanda ya yi nasara ba alƙalai ba,” inji Falana.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, ya wakilta ya ce yana fatan sakamakon taron zai taimaka wajen ci gaban Nijeriya.
Magajin garin Entebbe a Uganda, Fabrice Rulinda, ya ce dole ne Afirka ta bunƙasa salon dimokuraɗiyyar ta da zai yi aiki ga nahiyar, yana mai cewa ko a Amurka ba kowa ne ke zaɓen Shugaban Ƙasar ba.