Back

Yadda muka kuɓutar da ɗaliban Kuriga da aka sace a Zamfara, inji Sojoji

A ranar Lahadi ne Hedikwatar Rundunar Soji ta yi ƙarin haske kan yadda dakarunta tare da haɗin gwiwar jama’ar yankin suka kuɓutar da wasu ɗalibai sama da 137 da aka sace daga makarantar LEA Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a Kaduna.

Kuɓutar da ɗaliban na Kaduna ya zo ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan sojoji sun ceto ɗalibai 16 (Almajirai) tare da wata mata da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

An ruwaito yadda wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka sace ɗalibai da malaman makarantar su 287, waɗanda suka kai su daji, lamarin da ya tayar da hankula a faɗin ƙasar.

Bayan sace su, ‘yan ta’addan sun buƙaci a biya su kuɗin fansa naira biliyan 1 domin a sake su, inda suka tsayar da ranar 27 ga Maris, 2024 domin biyan su, yayin da suka yi barazanar cewa za su fara kashe su ɗaya bayan ɗaya idan ba a biya su kuɗin fansa a lokacin da suka ba da ba.

Da yake bayar da ƙarin haske da safiyar Lahadi, Daraktan Yaɗa Labarai na Ayyukan Tsaro, Manjo-Janar, Edward Buba, ya ce adadin waɗanda aka ceto ya kai 137, waɗanda suka haɗa da mata 76 da maza 61.

Babban jami’in sojan, wanda bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba, ya bayyana cewa sojojin sun haɗa kai da ƙananan hukumomi da hukumomin gwamnati a samamen da aka yi wa dazuzzukan Zamfara, inda a ƙarshe aka ceto su da sanyin safiyar Lahadi.

Amma bincike ya nuna cewa yaran makarantar Kuriga 150 har yanzu suna wurin masu garkuwan.

Yayin da sojojin suka miƙa waɗanda aka ceto ga gwamnatin jihar Sokoto, Buba ya ce yaran makarantar Kaduna da aka ceto su ma za a miƙa su ga gwamnatin jihar Kaduna.

Ya ce, “Za a iya tunawa cewa, a ranar 7 ga Maris, 2024, sojoji sun samu labarin cewa ‘yan ta’adda sun kai hari makarantar LEA Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. A lokacin da lamarin ya faru, an yi awon gaba da ɗaliban da ba a tabbatar da adadinsu ba.

“Bayan faruwar lamarin, sojoji sun yi alƙawarin cewa za su yi komai don kuɓutar da duk waɗanda aka yi garkuwa da su. A kan haka, a safiyar ranar 24 ga Maris, 2024, sojoji, tare da haɗin gwiwar ƙananan hukumomi da hukumomin gwamnati a fadin ƙasar, a wani aikin bincike da ceto, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Waɗanda aka yi garkuwa da su su ne waɗanda aka sace daga makarantar da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. An ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 137 da suka ƙunshi mata 76 da maza 61 a jihar Zamfara kuma za a miƙa su ga gwamnatin jihar Kaduna.”

Ya ƙara da cewa, nasarorin da sojojin suka samu a baya-bayan nan wata shaida ce ta ƙudirin da suka ɗauka na kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa ana yin irin wannan ƙoƙarin domin zaƙulo waɗanda suka kashe sojoji a jihar Delta.

“Waɗannan yunƙurin na nuni da ƙudirin da sojojin suka yi na gano sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba waɗanda aka yi garkuwa da su, tare da gano ƴan ta’addan da suka aikata waɗannan laifuka. Za a ci gaba da gudanar da wannan ƙoƙari har sai an samu sauran mutanen da aka yi garkuwa da su sannan kuma a kama ‘yan ta’addan, a yi musu shari’a, sannan a gurfanar da su a gaban kuliya bisa doka ta Nijeriya.

“Sojoji na yin irin wannan ƙoƙarin domin zaƙulo waɗanda suka kashe sojoji 18 a yankin Okuama da ke jihar Delta,” Buba ya ce cikin wata sanarwa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?