Back

Yadda na gaji bashin dala miliyan 587, naira biliyan 85, inji Gwamnan Kaduna

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana dalilin da ya sa albashin ma’aikatan jihar ya samu jinkiri a watan Maris, inda ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin da ta gabata.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wani taro a garin Kaduna a ranar Asabar, ya ce, duk da cewa bai ci bashin ko kwabo ba tun da ya hau mulki watanni tara da suka wuce, ɗimbin bashin da ake bin jihar yana cinye kason da Gwamnatin Tarayya ke ba wa jihar.

Ya ƙara da cewa daga cikin naira biliyan 10 da aka ware wa jihar a watan Maris, an cire naira biliyan 7 domin biyan basussukan.

Gwamna Sani ya koka da yadda farashin canji ya tashi, yanzu jihar Kaduna na biyan kusan sau uku na abin da tsohuwar gwamnatin Nasir el-Rufai ta karɓo.

Ya bayyana cewa, biyo bayan cire naira biliyan 7 don biyan bashin jihar a cikin watan Maris, an bar jihar da naira biliyan 3, wanda bai isa ya biya albashi ba, saboda lissafin albashin jihar na kowane wata ya kai naira biliyan 5.2.

Ya kuma tabbatar da cewa duk da basussukan da ake bin gwamnatin sa na ci gaba da jajircewa wajen ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba mai ɗorewa.

Gwamnan ya ce, “Duk da ɗimbin basussukan da suka kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 da muka gada daga gwamnatin da ta shuɗe, muna nan muna jajircewa wajen tafiyar da jihar Kaduna wajen samun ci gaba mai ɗorewa. Mun gudanar da cikakken nazari kan halin da muke ciki kuma muna ƙara ƙaimi a kan haka. Na yi farin cikin sanar da ku cewa, duk da ɗimbin bashin da muka gada a jihar, har yau ba mu ciyo ko kwabo ɗaya ba.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?