Back

Yadda Nijeriya ke asarar dala biliyan 3 a duk shekara sakamakon satar ma’adanai, inji masu haƙar ma’adinai

Masu ruwa da tsaki a fannin haƙar ma’adinai a Nijeriya a ranar Talata sun bayyana goyon bayansu ga kafa Tawaga ta Musamman kan Ma’adinai (SMSTF) don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a ƙasar.

Masu haƙar ma’adinan sun ce gwamnatin Nijeriya na asarar sama da dala biliyan 3 na kuɗaɗen shiga ta hanyar satar ma’adanai da ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Sun bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun masu ruwa da tsaki a harkar ma’adanai a ƙasar, Alhaji Mohammed Abba Liman, Babban Jami’in Kamfanin Daroo Nigeria Ltd, a Abuja, wanda ya zanta da manema labarai.

Liman ya ce: “Tawaga ta Musamman kan Ma’adinai (SMSTF), wadda mai girma Ministan Cigaban Ma’adanai, Dakta Dele Alake, ya kafa abin farin ciki ne.

“Yana da matuƙar muhimmanci domin zai rage matuƙa, idan bai daƙile ci gaba da satar ma’adinan mu da kuma ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ƙasarmu.

“Tattalin arziƙin Nijeriya yana asarar sama da dala biliyan 3 duk shekara saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya sa ‘yan Nijeriya da ‘yan ƙasashen waje ke haƙo albarkatunmu kamar zinari, tin, lu’u-lu’u, lithium da sauran duwatsu masu daraja ba bisa ƙa’ida ba tare da fitar da su wajen Nijeriya.”

Ya ce daga arewa maso yamma, arewa maso gabas, arewa ta tsakiya, da musamman kudu maso yamma, ana rage ma’adinan Nijeriya yadda masu aikata laifuka ke satar mai a yankin Neja Delta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?