Sojojin haɗin gwiwa sun samu nasarar dawo da gawarwakin sojoji 14 da aka kashe a rikicin ƙabilanci a jihar Delta.
Yunƙurin dawo da gawarwakin nasu ya kasance ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamandan Runduna ta 6 ta Nijeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam, a unguwar Okuama, a ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar.
Wasu daga cikin gawarwakin da aka gano an ce an sare kawunansu, yayin da aka cire kayan ciki da kuma zuƙatan wasu.
A Hukumar Raya Neja-Delta (NDDC), dake yankin gabar tekun Delta, an ga gawarwakin kwamandan jami’an da aka kashe da na Manjo biyu na shawagi a bakin kogin.
Tuni dai sojoji suka fara gudanar da bincike kan lamarin.