Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun ƙanin matarsa, wani Magaji Salisu saboda satar gishirin naira 20.
Ɗan marigayin, Ibrahim Zakari, wanda ya yi zargin, ya ce lamarin ya kai ga mutuwar mahaifinsa.
Ibrahim ya ce tashin hankalin ya fara ne a lokacin da mahaifinsa ya dawo daga kasuwa, sai matarsa Sadiya Salisu ta shaida masa cewa ta karɓi bashin gishirin naira 20, lamarin da ya fusata mahaifinsa da a baya ya yi gargaɗi game da karɓar kowane irin bashi daga wurin kowa.
Ibrahim ya ce rigimar da ta faru tsakanin marigayin da matarsa ta kai ga yin musayar kalamai.
Ɗan ya ce mahaifinsa ya koma shagonsa ya kira ɗan uwan matarsa a waya ya shaida masa duk abin da ya faru a gida tsakaninsa da matarsa.
An yi zargin cewa ɗan uwan matar ya fusata ya zo gidan yana neman mijin ‘yar uwarsa amma bai same shi a gida ba, ya yanke shawarar bin shi zuwa shagonsa da ke ‘Yan shinkafa a Kura.
Ɗan marigayin ya ƙara da cewa, Magaji na ganin mahaifinsa, sai ya fara dukansa bayan da ƙashin kirjinsa ya karye.
Ya ce sun kai mahaifinsu wani asibiti da ke kusa da garin Kura inda likita ya yi masa magani ya sallame shi amma ya ce bayan sun koma gida mahaifinsa ya rasu.
Ibrahim ya ce sun kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda kuma DPO na Kura ya gayyaci matar da ɗan uwanta kuma yanzu haka suna hannun ‘yan sanda.
Ya roƙi Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kano da ya tabbatar wa mahaifinsa adalci. Babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan jihar kan lamarin.