Back

Yahaya Bello ya musanta biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa da kuɗaɗen gwamnati

Yahaya Bello

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ƙaryata zargin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi masa na cire kudi dalar Amurka 720,000 ko kuma “dala 840,000 da ake yaɗawa a yanar gizo” daga asusun Gwamnatin Jihar Kogi domin ya biya kuɗin makarantar ‘ya’yansa, daf da barin ofis.

Shugaban EFCC, a wata zantawa da manema labarai, ya yi zargin cewa Bello ya cire dala 720,000 daga asusun gwamnati domin biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa na nan gaba.

A wata sanarwa ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun Ohiare Michael na ofishin yaɗa labarai na Bello, tsohon gwamnan ya ce bai biya kuɗin makarantar ‘ya’yansa da kuɗaɗe daga asusun Gwamnatin Jihar Kogi ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Yaran Mai Girma Yahaya Bello sun halarci makarantar American International School da ke Abuja tun kafin ya zama gwamna kuma ya biya wa ‘ya’yansa kuɗaɗen makaranta a lokacin da ya dace ba tare da gazawa ba.

“Mai Girma Gwamna, Alhaji Yahaya Bello bai biya dala 720,000 ba kamar yadda Shugaban EFCC ya yi zargi ko kuma dala 840,000 kamar yadda ake yaɗawa a yanar gizo.

“Ba a biya kuɗaɗen ba a daidai lokacin da mai girma zai bar ofis kamar yadda Mista Olukoyede ya yi iƙirari amma an fara hakan a shekarar 2021.

“Alhaji Yahaya Bello bai biya wa ‘ya’yansa kuɗaɗe daga asusun Gwamnatin Jihar Kogi ba.

“Lokacin da EFCC ta tunkari American International School Abuja (AISA) domin ta ƙwato kuɗaɗen da Alhaji Yahaya Bello da sauran ‘yan uwa suka biya ba bisa ƙa’ida ba, wani ɗan gidan ya ƙalubalanci ayyukan hukumar EFCC da ta aikata ba bisa ƙa’ida ba na ƙwato kuɗaɗen da aka biya bisa doka.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?