Back

‘Yan bindiga a Katsina sun saki wani bidiyo mai ban tsoro bayan sun yi garkuwa da mata 63 da ke rakiyar amarya

Yan bindiga a Katsina sun saki wani faifan bidiyo mai daure kai da ban tsoro bayan sun yi garkuwa da mata sitting da uku a lokacin da suke rakiyar amarya ranar Jumma’at da ta gabata. 

A wani al’amari mai daure kai da ban tsoro, ‘yan bindigan da suka yi kaurin suna a jihar Katsina wadanda suka sace mata 63 ranar Juma’a da ta gabata a yayin da suke rakiyar wata sabuwar amarya zuwa gidan mijin ta sun fitar da wani faifan bidiyo mai tada hankali.

Masu laifin sun nuna rashin kunya sun bayyana aniyarsu ta “sake aurar da amaryar.” 

Bidiyon da ake yadawa a dandamali dabam-dabam, musamman na sada zumunta, ya nuna bajintar ‘yan fashin yayin da suke bayyana laifukan da suke aikatawa.

A cikin kalaman da suka yi, masu garkuwar na nuni da wata mummunan makoma ga matan da aka yi garkuwa da su.

Hukumomin yankin da jami’an tsaro na ci gaba da yin tattaki don shawo kan lamarin, inda mazauna yankin suka nuna bacin ran su game da wannan aika-aikar da ‘yan fashin suka nuna a fsifan bidiyon.

Fitar da irin wannan faifan bidiyo ya karawa dangi da sauran al’umma damuwa game da tabarbarewar tsaro a yankin, lamarin da ya sa ake kira da a dauki matakin gaggawa domin ganin an dawo da matan da aka sace cikin koshin lafiya tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Lamarin ya kara jaddada bukatar karfafa matakan tsaro cikin gaggawa da kuma kokarin hadin gwiwa domin dakile matsalar ‘yan fashi a jihar Katsina.

Yayin da al’umma ke jiran sabbin bayanai kan binciken da ake yi da kuma kokarin ceto wadanda aka sacen, faifan bidiyon Wanda ke cike da ban tausayi ya zama abin tunatarwa kan kalubalen da ake fuskanta wajen yakar aikata laifuka a yankin.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?