Ɗaruruwan mutanen ƙauyen Bini da ke ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara sun taru a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Lahadi, inda suke neman gwamnati ta kare su daga ‘yan bindiga.
Mazauna ƙauyen waɗanda akasari mata da ƙananan yara ne sun ce sun tsere daga ƙauyukan su ne biyo bayan janyewar jami’an soji daga yankin.
Ɗaya daga cikinsu mai suna Malam Umar Salisu ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa dole ne ya sa suka gudu daga ƙauyensu biyo bayan janyewar jami’an soji daga yankin.
“A da, akwai jami’an soji da ke aiki a ƙauyenmu. Wasu daga cikinsu ‘yan bindiga ne suka kashe su yayin da aka janye wasu a ranar Lahadi. Yanzu dai babu jami’an tsaro a yankinmu. Shi ya sa muka yanke shawarar kai dukkan matanmu da ‘ya’yanmu gidan gwamnati domin neman taimakon gwamnati,” inji Salisu.
Wata ‘yar ƙauyen da ta gudu, Hajiya A’isha Usman, ta bayyana rashin jin daɗinta kan halin da al’ummar yankin suke ciki.
“Mun damu matuƙa. Muna samun barazanar kai hare-hare daga ‘yan bindiga kullum. Babu jami’an tsaro da za su kare mu. Muna neman sa hannun gwamnati, ” inji ta.
A lokacin ziyarar mutanen ƙauyen, Gwamna Dauda Lawal baya gidan gwamnati.
An ce ba ya ƙasar ne, ya halarci wani taro, tare da wasu gwamnoni shida na Arewa-maso-Yamma, a ƙasar Amurka.
Da yake jawabi a madadin gwamnatin jihar, Kwamishinan Kimiya da Fasaha na Jihar, Alhaji Wadatau Madawaki, ya bayyana cewa ‘yan bindigar na ƙara matsa lamba ne saboda gwamnati ta ƙi tattaunawa da su.
Madawaki ya ƙara da cewa gwamnati ta yi shirin mayar da mutanen ƙauyen da suka gudu cikin al’ummarsu tare da jami’an tsaro.