Back

‘Yan bindiga sun buƙaci naira biliyan 1 na ‘yan makarantan Kaduna 287 da aka sace

Ƙasa da sa’o’i 24 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce ba za a biya kuɗin fansa na waɗanda aka sace ‘yan makaranta sama da 287 a ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ba, rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun buƙaci a biya su kuɗin fansa naira biliyan ɗaya daga iyalan waɗanda abin ya shafa.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Shugaba Tinubu ta bakin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya yi watsi da yiwuwar biyan kuɗin fansa domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a ƙasar.

Ya kuma umurci jami’an tsaro da su yi abin da ya kamata don ceto yaran da suka haɗa da ɗaliban makarantar allo na Sakkwato da ‘yan gudun hijira a jihar Borno.

An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi kira domin neman kuɗin fansa da suka ce a biya su cikin kwanaki 20 masu zuwa.

Ɗaya daga cikin shugabannin matasan yankin, Aminu Kuriga, wanda ya tabbatar da kiran wayar, ya shaidawa jaridar cewa mutanen sun damu matuƙa.

“’Yan bindigar sun yi iƙirarin cewa suna wani wuri a arewacin Zamfara tare da yaran kuma mu biya Naira biliyan 1 kafin kwanaki 20 masu zuwa.

“Sun samu lambar waya ta ta hannun shugaban makarantar, Abubakar Isah, da aka sace, wanda ya kasance abokina ne na ƙuruciya. Muna addu’ar Allah ya kawo mana ɗauki kan wannan lamari,” inji shi.

An ruwaito yadda ‘yan bindigar suka mamaye makarantar da safiyar Alhamis ɗin da ta gabata jim kaɗan bayan kammala taron safiya inda suka yi awon gaba da ɗaliban da wasu ma’aikatan makarantar.

Gwamnan jihar Uba Sani, ya ziyarci al’ummar sa’o’i bayan an yi garkuwa da su, ya kuma tabbatar wa da iyayen cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa duk ‘ya’yansu sun dawo ba tare da wani rauni ba.

Sai dai kwanaki bayan faruwar lamarin, ba a samu labarin an ceto wani yaro a cikin al’ummar ba, har ma an ga ‘yan bindigar a ƙofar shiga unguwar bayan kwanaki biyar da satar makarantar.

Gwamnatin jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan buƙatar kuɗin fansa ba.

An kasa samun Komishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin gida, Samuel Aruwan, ta wayar tarho kuma bai amsa saƙon WhatsApp da aka aika masa ba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?