’Yan bindigan da suka karbi Naira miliyan 8.5 kafin su sako mutane hudu daga cikin mutane 17 da suka hada da wata ma’aikaciyar jinya a Kawu da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja, sun sake neman sabbin baburan Bajaj guda biyu domin su sako sauran mutum 11 da aka yi garkuwa da su.
‘yan bindiga sun mamaye kauyen Kawu a ranar 26 ga Disamba, 2023, ne tare da yin garkuwa da mutane 23. Hudu daga cikinsu sun tsere, inda suka bar wasu 17 a hannun ‘yan ta’addan. An ce barayin sun yi barazanar kashe sauran 11 da suka rage saboda jinkirin kawo kudin fansa.
Da yake magana da wakilan Jaridu a ranar Juma’a, wani daga cikin dangin daya daga wadanda abin ya shafa, Bala Dantani, ya ce an biya kudin fansar kashi-kashi ne. Ya ce an tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 5, aka mika wa ‘yan bindigar, bayan da suka yi barazanar kashe wadanda suka yi garkuwa da su makonni biyu da suka wuce.
A cewarsa, an kai Naira miliyan 3.8 ga barayin a ranar Talata, da suka hada da kayan abinci da magunguna da kuma giya, bayan da shugaban ya yi alkawarin sakin wadanda abin ya shafa.
“Kuma a lokacin da ake jiran kiran nasu domin bayyana mana wuraren da za mu dauko wadanda abin ya shafa a ranar Talata, mutumin da ya Kai kudin fansar, da ya dawo yace ‘yan bindigarn sun sake neman babura biyu kafin su sako sauran 11.” inji shi