Wasu ‘yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhammad Bunu, inda suka kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin.
‘Yan bindigar waɗanda suka kai farmaki garin da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Laraba, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, sun kuma kai hari gidan tsohon shugaban mulkin soja na Jihar Nasarawa, Kanar Bala Muhammad Mande (mai ritaya).
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa, da isar su garin, ‘yan bindigar sun nufi fadar sarkin ne kai tsaye suka buɗe wuta a ƙofar shiga fadar don su samu damar shiga.
Ya ce: “An kulle ƙofar, idan ba haka ba, da sun samu shiga cikin fadar, wataƙila har su isa wurin sarkin. Don shi suka kai harin domin sun yi yunƙurin sace shi ba da daɗewa ba.
“Ya dawo garin ne a ranar Litinin bayan yunƙurin farko na sace shi ya ci tura. Sarkin ya koma babban birnin Jihar, Gusau, inda ya shafe mako guda a can,” inji majiyar.
Wani mazaunin garin, wanda shima ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a lokacin da ‘yan bindigar suka kasa samun damar shiga fadar, sai suka koma gidan tsohon jami’in sojan, inda suka yi harbi da dama a ƙofar gidan.
“A hanyarsu ta fita daga garin sun kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu. Ba mu san adadin mutanen da aka sace ba domin lokacin da ‘yan bindigan suka fara harbin, mazauna yankin sun ruga cikin daji domin tsira.
“Babu wanda ya tsaya lokacin da ‘yan bindigar ke harbin bindiga. Harbe-harben na da ban tsoro, don haka, duk muka gudu cikin daji don tsira da rayukanmu.
“Muna kira ga gwamnati da ta samar da isassun sojoji a garin domin ‘yan bindigar na iya sake dawowa tunda sun san sarki yana garin. Abin da suke so shi ne su sace sarkin kuma ba mu san dalilin da ya sa suke son sace shi ba,” inji mazaunin garin.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce bai da masaniyar cewa an kashe wasu mutane.
Sai dai CP Dalijan ya amince cewa ‘yan bindigar sun sace ɗaya daga cikin ma’aikatan fadar Sarkin Zurmi.
“Ba a sace shi a fadar ba kamar yadda ake hasashe. An sace shi ne a wani wuri a cikin garin.
“Zan iya tabbatar da sace mutum ɗaya kawai da kuma ƙona sabis na waya,” inji shi.