A safiyar yau Alhamis ne ‘yan ta’adda suka kai hari gidan Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, Alhaji Musa Mallaha, a Gusau, inda suka kashe ɗansa da mai gadi.
‘Yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da wani ɗansa.
Wani mazauni a unguwar ya shaidawa jaridar Blueprint cewa sun fasa babbar ƙofar gidan a yayin harin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun so su sace Shugaban ne amma basu yi nasara ba inda daga bisani suka kashe ɗansa da mai gadi tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ke zaune a gidan.
“Mun ji ‘yan ta’addan suna ta harbe-harbe amma bayan sun tafi sai muka gano cewa sun kashe Abdulmunaf tare da yin garkuwa da ɗan uwansa Mu’awiya Lawali Mallaha da mai gadinsa.”
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba a yayin harin da aka kai a garin.
Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Asp Yazid Abubakar, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa rahoton.