Back

‘Yan bindiga sun kai hari kasuwar Neja, sun kashe hakimin ƙauye, da wasu 20 da rana tsaka

Aƙalla mutane 21 ciki har da hakimin ƙauyen ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata kasuwa da ke Madaka, wata ƙauye a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce maharan sun kai farmaki kasuwar ne da misalin ƙarfe 3 na rana a lokacin da ake gudanar da harkokin kasuwanci inda suka fara harbe-harbe kan jama’ar.

An ce mutane da dama sun samu raunuka daban-daban kuma suna karɓar magani a Asibitin Ƙwararru na IBB da ke Minna.

An kuma ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane da dama da suka haɗa da yara yayin da aka ƙona babura, motoci, gidaje, shaguna da kayayyakin ‘yan kasuwa.

Mazauna yankin sun ce harin na Madaka ya zo ne kwana guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Pangu Gari da ke maƙwabtaka da ƙauyen, inda suka kashe hakimin gundumar da wasu mutane huɗu.

Majiyoyi sun ce bayan harin da rana, ‘yan bindigar sun dawo cikin dare inda suka yi wa al’umma kawanya, suna harbe-harbe.

Majiyoyi sun yi zargin cewa maharan na shirin ƙwato shanun da aka ƙwato daga hannunsu a wani samame ta sama da aka yi a yankin tare da yin awon gaba da wasu dabbobi.

Hakimin Gundumar, Alhaji Isah Bawale ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Sakataren Haɗakar Ƙungiyar Shiroro, Saidu Salihu ya bayyana harin a matsayin mai muni da rashin tausayi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su sabunta ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da rashin tsaro a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi.

Mazauna yankin sun kuma yi tir da rashin halartar jami’an tsaro duk da cewa an sha kai hare-hare a yankin sau da dama a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya) ya tabbatar da harin ta wayar tarho.

Ko da yake bai bayar da cikakken bayani kan harin ba, ya ce gwamnatin jihar na aiki tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa manoma a jihar.

Da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alƙawarin mayar da martani da cikakken bayani.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?