Back

‘Yan bindiga sun kai hari shingen binciken ababen hawa, sun kashe ‘yan sanda huɗu da wasu mutane biyu

Wasu ‘yan bindiga sun harbe jami’an ‘yan sanda huɗu a ranar Juma’a a garin Abakaliki na jihar Ebonyi a wani hari da suka kai a wani shingen bincike. An kuma ce an kashe mata biyu a harin.

Shingen binciken da aka kai harin na kusa da wata tashar iskar gas da ke kusa da gadar Ebya da ke kan titin Hilltop/ Nwoke.

Wannan shi ne hari na biyu da aka kai kan shingen binciken – na farko wanda ya faru a bara ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.

Titin babbar hanya ce ta shiga cikin birnin kuma tana kaiwa gidan gwamna Francis Nwifuru.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Joshua Rukandu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce jami’an ‘yan sandan na kan aikin bincike ne a lokacin da aka kai musu farmaki.

Ya ce ana zargin maharan da kasancewa ‘yan Ƙungiyar Tsaro ta Gabas, reshen ƙungiyar masu fafutukar neman kafa ƙasar Biafra (IPOB).

Mista Trikandu ya ce ‘yan bindigar da jami’an sun yi ta musayar wuta.

Ya ƙara da cewa, “A faɗan da ya biyo baya, ‘yan bindigar sun tsere inda suka yi watsi da wata bindiga. Sai dai an kashe huɗu daga cikin jami’an, yayin da musayar wutar ta ritsa da wasu fararen hula biyu kuma suka mutu.”

Mai magana da yawun ya ce, ‘yan sandan na bin ‘yan bindigar ne bayan da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi, Augustina Ogbodo, ya aika wata tawaga cikin gaggawa zuwa inda aka kai harin.

Ya ƙara da cewa, “Tana amfani da wannan kafar wajen yin kira ga ‘yan jihar nagari da su baiwa hukumar bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen kama ‘yan ta’addan da suka gudu tare da ba da tabbacin cewa rundunar ta ci gaba da sadaukar da kai don kare rayuka da dukiyoyi a jihar,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?