Back

‘Yan bindiga sun kashe jami’an Rundunar Haɗin Gwiwa ta Farar Hula 9, sun yi garkuwa da mutane 3 a Sokoto

Aƙalla jami’an Rundunar Haɗin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) guda tara da ke yaƙi da ‘yan bindiga a Jihar Sokoto ne aka kashe a wani harin kwantan ɓauna da aka kai musu, yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka daban-daban.

An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kuma tafi da wasu jami’an CJTF uku.

Wata majiya ta shaida cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Isa ta jihar.

Majiyar CJTF ta ƙara da cewa ƙaramar hukumar Isa ta kasance tungar ‘yan bindiga kuma tana da matuƙar haɗari ga jami’an tsaro.

“Mun rasa jami’ai tara a wani harin kwantan ɓauna da aka kai a ƙaramar hukumar Isa, wasu da dama sun samu raunuka, an kuma yi awon gaba da wasu guda uku a harin bayan da jami’an mu suka samu kiran gaggawa na tallafa wa jami’an tsaro.

“Mun samu labarin baƙin cikin kwanaki biyu da suka wuce. Tun farkon wannan shekara gwamnatin jihar ta buƙaci mu tura jami’an mu domin tallafa wa sojoji a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga a yankin Arewa-maso-Yamma.”

Ku tuna cewa wannan shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga za su yi wa jami’an CJTF kwanton ɓauna a Jihar Sokoto cikin watanni biyu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?