Back

‘Yan bindiga sun kashe Mai’unguwa a Kaduna, sun ƙona gidansa

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Malam Kabiru Mohammed, Mai’unguwan Marke da ke yankin Dandamisa a ƙaramar hukumar Maƙarfi a Jihar Kaduna.

‘Yan bindigar waɗanda ake zargin hayar su aka yi, sun shiga gidan mamacin ne da misalin ƙarfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis inda suka kori kowa daga harabar gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa sun fara neman Malam Kabiru wanda ke ɓoye a cikin silin tare da ƙanensa Tukur Mohammed.

A cewar wani ɗan unguwar da ya nemi a sakaya sunansa, daga bisani ‘yan bindigar sun gano wanda abin ya shafa inda suka yanka shi suka banka masa wuta.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kansilan unguwar Dandamisa, Alhaji Aminu Sani Marke, ya ce ba a iya gano gawar marigayin ba saboda ƙonewar gidan.

Ya ce, “’yan bindigar sun shafe kusan awa ɗaya suna gudanar da aiki a ƙauyen, inda suka tafi da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin naira.”

Marigayi Kabiru Muhammad, mai shekaru 30, an naɗa shi a matsayin Mai’unguwan garin Marke a shekarar 2018.

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?