Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba sun kashe wani makiyayi ɗan shekara 17 da shanu 35 a unguwar Nafan da ke gundumar Fan da Doruwa Babuje a gundumar Ropp da ke ƙaramar hukumar Barkin-Ladi a jihar Filato.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa waɗanda suka aikata laifin suna kan babura ne a lokacin da suka buɗe wuta tare da kashe makiyayin.
Wani makiyayi kuma ya samu munanan raunuka a yayin lamarin.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar wanda ya yi Allah wadai da lamarin, ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na sa, Mista Gyang Bere, ya fitar ranar Alhamis a Jos.
Mutfwang ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani aiki na rashin bin doka da oda ba ko kuma kisan gillar da ake yi wa ‘yan ƙasa da ba su ji ba su gani ba, masu bin doka da oda.
“Muna yin Allah wadai da waɗannan ayyukan rashin bin doka da oda da ke kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati na samar da zaman lafiya a jihar.
“Gwamnatina ba za ta ci gaba da lamuntan kisan gilla da ake yi wa ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba, ko dai a gonakinsu ko kuma a duk sassan jihar, yayin da suke neman na abincin su.
“Na umurci hukumomin tsaro da su farauto tare da zaƙulo waɗanda suka aikata waɗannan munanan laifuka tare da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa,” inji Gyang Mutfwang.
Gyang ya ƙara da cewa, gwamnan ya yi kira ga shugabannin gargajiya, al’umma, da na addini, da ƙungiyoyin matasa da mata na al’ummomin da abin ya shafa, da su haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin.
Gwamnan, wanda ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, ya shawarci mazauna jihar da su tona asirin duk masu aikata laifuka a cikin al’ummar su domin su fuskanci fushin doka.