Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyuka biyu na manoma a Jihar Zamfara, inda suka kashe manoma aƙalla 30, har da wani fitaccen malamin addinin Islama.
A wani wuri kuma a Filato an kashe makiyaya biyu da shanu sama da 200.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar harin a wasu ƙananan hukumomi biyu na jihar, sai dai ya ce nan gaba za a bayar da cikakken bayani.
Majiyoyi sun shaida cewa lamarin ya faru ne a Jihar Zamfara a ranar Alhamis.
Wata kafa ta yanar gizo, PR Nigeria, ta ruwaito cewa an kai harin ne a ƙananan hukumomin Maradun da Tsafe.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa an kashe Malam Makwashi Maradun Mai Jan Baki, fitaccen malamin addinin Islama da wani mutum a garin Maradun.
Biyu daga cikin yaran malamin har yanzu ba a gansu ba bayan harin.
An samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kashe wasu mutane uku a ƙauyen Gidangoga, yayin da mazauna ƙauyen suka kashe ‘yan bindiga 24 tare da ƙwato babura takwas.
Wani mazaunin Maradun ya ce: “Mun yi artabu da ‘yan fashin sosai. Hare-hare dai na ci gaba da ruruwa a yankin Maradun a ‘yan kwanakin nan. Suna faruwa kusan kowace rana. An kori al’ummomi da dama a ƙaramar hukumar saboda tsoron ɗaukar fansa.”
Kazalika PR Nigeria ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyen Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka kashe fararen hula 20.
Majiyoyin yankin sun ce an kai wa manoma hari ne a lokacin da suke share gonakinsu, kuma ‘yan fashin ba su nuna tausayi ba.
An kuma ruwaito cewa wani hakimi mai suna Alhaji Murtala Ruwan Bado na Garbadu a Masarautar Talata Mafara shi ma da ƙyar ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ‘yan bindiga suka kai musu a yammacin ranar a kan hanyar Mayananchi.
A Jihar Filato, an ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe makiyaya biyu da shanu sama da 200 a wani harin da suka kai a gundumar Kwal da ke ƙaramar hukumar Bassa.
A cewar shugabancin Fulani a jihar, an kuma sace shanu sama da 100 a lokacin da lamarin ya faru.
Shuwagabannin Kungiyar kasashen Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN), Nura Abdullahi da Garba Abdullahi ne suka tabbatar da faruwar lamarin a jiya.
Da yake bayyana lamarin, Shugaban GAFDAN ya ce: “Makiyayan suna kiwon shanunsu da misalin ƙarfe tara na safiyar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka bayyana suka fara harbi.
“Sun harbe makiyaya biyu har lahira. Sun kuma harbi sama da shanu 200. Har yanzu dai ba mu iya tantance yawan ɓarnar ba saboda lamarin ya faru ne a wani wuri mai nisa da ke da wahalar shiga ba tare da jami’an tsaro ba. Mun yi babban rashi.
“Lokaci ya yi da jami’an tsaro za su ɗauki mataki kan ta’asar da ake yi wa mutanen mu. A duk lokacin da aka kai mana hari, jami’an tsaro suna neman mu kwantar da hankalinmu. Wannan yunƙuri ne na halaka mu, kasancewar harin da ba gaira ba dalili ne. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kawo mana agaji,” inji Garba.